Ana ganin ‘yan bindigar na Zamfara yaran Buharin Daji (mai rike da lasifika) ne, wanda aka kashe farkon watan Maris ke ci gaba da aikata fashi

Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, ta ce ta gudanar da wani zama da wasu tsofaffin ‘yan fashin daji domin kawo karshen rikici na baya-bayan nan da ya sake kunno kai.

Wasu rahotanni na cewa rikicin ya yi sanadin kashe sojoji guda tara a yankin Anka.

Bayanai sun ce ‘yan fashin daji sun auka wa sojojin da ke aiki a kauyen Sunke na karamar Hukumar Anka a karshen makon jiya.

Kafin ‘yan makwannin nan, jihar Zamfara ta sha fama da rikicin ‘yan fashin daji, wadanda suka yi kaurin suna wajen satar mutane don neman kudin fansa da washe kauyuka da fashi da makami.

A tattaunawarsa da BBC babban mataimaki na musamman ga gwamnan Zamfara kan harkokin tsaro, Alhaji Abubakar Dauran ya ce sun yi taron ne tare da shugabannin tsaro na soji da ‘yan sanda da kuma shugabannin Fulani domin gano bakin zaren.

“Mun zauna da shugabannin Fulanin da suka zubda makamansu, kuma sun tabbatar mana da cewa ba su da hannu a wannan hari.”

Ya kara da cewa, “Domin haka wadanda suka kai wa sojojin hari wasu bata gari ne na wata kungiyar daban, kuma gwamnati za ta dauki matakin ba sani ba sabo don hukunta wanda aka samu da laifi”, inji Alhaji Abubakar Dauran.

Ya kuma ce “Rahotanni sun ce an kashe sojoji tara, sannan wancan bangaren na ‘yan fashin dajin suma an kashe mutum 19. Amma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, muna shaidawa jama’a cewa hankula sun kwanta an ci gaba da gudanar da al’amura yadda ya kamata a karamar hukumar Anka da kewaye”.

Lamuran tsaro sun fara daidaita a jihar Zamfara tun bayan hawan Alhaji Bello Matawalle kan karagar mulki, barayin daji sun hau teburin sasantawa da gwamnati wanda ake ganin ya yi tasirin tabbatuwar zaman lafiya a jihar.

SANARWA! GobirOnline.com na bukatar Karin ma’aikata (Voluntary), kwararru, ta fannin watsa Labarai, Tarihi, wasanni da Al’adu, Domin bunkasa ayukkan wannan shafin.

CONTACT US

We're not around right now. But you can send us an email and we'll get back to you, asap.

Sending

©2019 GobirOnline  all right received | Arewa-community | G. D. A.

or

Log in with your credentials

or    

Forgot your details?

or

Create Account