A wani nazari da  LEGIT.NG ta yi ta gano yawaitar rabuwa tsakanin masoya, musamman a yankin kasar Hausa.

Idan kana mamakin yadda aka yi budurwarka ta rabu da kai, watakila kana bukatar yin tunani da irin soyayyar da ke tsakanin ka da ita. Yi la’akari da wasu dalilai wadanda ‘yammata da yawa ba sa so, wanda zai iya kawo karshen soyayyarku.

Soyayya ta gaskiya, ta na bukatar yarda da juna, da kuma hakuri ta kowacce hanya.

Amma idan ka aikata daya daga cikin wadannan kurakuran, to akwai yiwuwar soyayyarku ta kusa zuwa karshe.

1. Rashin sannin yadda zaka tarairayi budurwarka, ko ka dinga saka ta farin ciki.

2. Babu abinda ka iya sai tura mata sakonni ta waya, eh an yadda cewa sako yana da amfani a wasu lokutan. Amma kuma idan har tattaunawar da zaku yi ta na da yawa, abinda ya kamata kayi shine ka kirata.

3. Ba ka bata hakuri idan kayi mata laifi.

4. Rashin fada mata kalaman soyayya, da yawan ‘yammata suna son kalaman soyayya, suna so saurayi ya dinga koda su.

5. Yawan yi mata karya, maza da yawa suna yi wa ‘yammata karya, suna ganin kamar ‘yammata sun fi kaunar mutum idan ya yi musu karya. Hakan ba dai dai bane saboda duk ranar da ta gano ka, to karshen soyayyarku ya zo kenan.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

6. Rashin damuwa da sanin abokanta. Ba dole sai ka so abokananta ba, amma ya na da kyau ka girma alakar da ke tsakaninta da su, ya kamata su ma ka girmama su, saboda sune ginshikin soyayyarku a wasu lokutan.

7. Ba ka yi mata tambayoyi idan ta na magana da kai, yin shiru idan ta na magana ya na da kyau, saboda ya na nuna mata cewa hankalinka ya na wurinta, amma kuma rashin yi mata tambayoyi shi ma wata matsala ce a wurinta.

8. Rashin buri a rayuwa. Babu wata mace da ke son namiji wanda ba shi da buri a rayuwarsa.

9. Yawan ba ta uzuri, irin su, baka tashi da wuri ba, cunkuso ya rike ka da dai sauransu, mata ba sa son irin wannan uzurin.

10. Yawan yi mata maganar tsohuwar budurwarka. Duk namijin da ya fiya yiwa mace maganar tsohuwar budurwarsa, to ya tabbata cewa soyayyarsu ta kusa karewa da budurwarsa.

©2020 GobirOnline  all right received | Arewa-community | G. D. A.

CONTACT US

We're not around right now. But you can send us an email and we'll get back to you, asap.

Sending

Log in with your credentials

or    

Forgot your details?

Create Account