Masana sun gano yadda dan adam zai samu tsawon rai

Nasarar da masanin kimiya dan kasar China ya samu ta sauya kwayoyin halittar wani jinjiri a cikin watan nuwamban da ya gabata, na ci gaba da bai wa sauran masana kwarin gwiwar cewa, abu ne mai yiyuwa a samu nasarar sauya kwayoyin halittar dan adam, wanda hakan zai ba shi damar yin rayuwa tsawon shekaru a duniya.

Masana na ganin cewa, samun nasarar gudanar da bincike domin sauya wasu daga cikin kwayoyin halittar dan adam, da suka hada da yin dashen kwakwalwa da tsawaita shekarun da mutun zai rayu a duniya da dai sauransu, wadannan abubuwa ne da za su iya yiyuwa nan ba da jimawa ba.

To sai dai nasarar binciken da wani dan kasar China mai suna He Jianjui ya yi ta fannin samar da jinjiri na farko da aka sauyawa kwayoyin halitta tare da hana shi kamuwa da kwayar cutar HIV a duk tsawon rayuwarsa, lamari ne da ya haddasa cece-ku-ce a tsakanin masana.

Yanzu haka dai kamfanonin da suka shahara ta fannin kimiya da fasaha a duniya irinsu Google da Tesla da kuma Calico, sun fara bayyana shawarsu ta ganin cewa sun bayar da tasu gudunmawa domin samun nasarar irin wannan bincike.

A cikin shekarun baya-bayan nan dai, ana samun raguwar shekarun da mutane ke rayuwa a Amurka, abin da ya kara zaburar da masana domin fara bincike a wasu jami’o’i da nufin gano yadda za a magance wannan matsala, kuma hanya daya ce masanan ke ganin cewa za a iya amfani da ita, wato sauya kwayoyin halittar dan Adam.

Share This Post
Have your say!
00

Customer Reviews

5
0%
4
0%
3
0%
2
0%
1
0%
0
0%

Leave a Reply

Thanks for submitting your comment!