Makamin Kare dangi (Nuclear weapons)

Minene Makamin Kare dangi (Nuclear weapons)?
Cecekuce da ake ta yi kan kasashe irin su Koriya ta Arewa da kasar Iran ko Farisa a yau ya samo asali ne daga shirinsu na mallakar wani makamin tsare kasa da ake kira makamin nukiliya, ko kuma nuclear weapon, a harshen Turanci. Wadannan kasashe, kamar sauran kasashe ‘yan uwansu, na da hakkin kare kasashensu da duk irin makamin da suka ga ya dace, musamman dangane da irin tsarin da duniya ke gudanuwa a kai a yau ; na yaudara da gilli da kinibibi da munafunci. To amma saboda wasu tsare-tsare da ake ganin sun zama dole a yi, wai don duniya ta samu zama lafiya, ta fita daga halin zaman dardar da ta shiga lokacin yakin cacan-baki (cold war), ake ganin ya zama dole kowace kasa ta rattafa hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar mallaka da kuma amfani da wannan makami mai suna makamin nukiliya. Wai shin, me ke kunshe cikin wannan makami ne da har ake kokarin hana wasu mallakarsa? Ya sha bamban ne da sauran makamai ta wajen barna, ko kuwa? In haka ne, to me yasa wasu suka mallaka wasu kuma aka hana su mallaka? Me yasa wasu suka bata nasu?Kasashe nawa suka mallaki wannan makami?Yaya tasirin wannan makami yake wajen murkushe rayuwa da lafiyar dan Adam da muhallinsa? Wadannan, da ma sauran tambayoyin da masu karatu zasu karanta nan gaba, na kumshe cikin wannan silsila da zamu fara a yau in Allah ya yarda. Da farko dai, ga ma’ana da nau’ukansa da kuma yadda aka yi wannan makami ya samo asali a duniya:

Ma’ana da Nau’ukan Makamin Nukiliya

Makamin Nukiliya, ko Nuclear Weapon a turance, wani irin makami ne mai karfi da saurin fashewa sanadiyyar wasu sinadaran kimiyya masu tarwatsewa ko harhadewa da junansu don haifar da makamashin madda (atomic energy) a yanayin hayaki ko haske mai dauke da tururin guba ga lafiya ko rayuwar dan Adam da muhallinsa. Idan makamin nukiliya ya fashe a wuri ko gari misali, dole a samu karar fashewa mai tsananin firgitarwa, wacce ke biye da hayaki mai guba gad an Adam ko wasu halittu, tare da wuta mai ci balbal, a karshe kuma, akwai tururin haske mai cutarwa idan ya hadu da maddar muhalli.Wannan tururin haske mai cutarwa da a ilimin kimiyya ake kira radioactive radiation, mai cikakken hadari ne ga fatar jiki da lafiya ko ran dan Adam, kuma yana iya kasancewa a dukkan ilahirin wurin da aka samu wannan fashewa na tsawon shekaru. Da kasar wurin, da iskar wurin duk zasu gurbata. Idan mizanin wannan makami ya kai tan miliyan a misali, karfin fashewarsa na iya haddasa ‘yar karamar girgizar kasa a ‘yan takaitattun taku daga wurin da fashewar ta auku.

Manyan sinadaran kimiyyar da ake amfani dasu wajen kera wannan makami a duniya su ne makamashin fulutoniyon (plutonium) da kuma yuraniyon (uranium). Ana dafa su ne har su kai wani mizani na zafi wanda ke canza hakikaninsu zuwa wasu maddodin dabam, ya kuma basu tasirin fashewa ko hadewa da juna, sanadiyyar alakarsu ko kusancinsu da wasu makamashin haske ko maddodin dabam. Saboda tsananin tasirinsa ga muhalli, tan guda na makashin nukiliya da ke dauke cikin makami ko kwansonsa, idan aka harba shi, tasirin fashewa da kara da yawan sinadaran da zai fitar, daidai yake da tasirin fasa bam irin na zamani guda biliyan daya, a lokaci daya, kuma a wuri daya. Idan kuma aka samu fashewar makamin nukiliya da mizaninsa ya kai tan dubu ko sama da haka, to yana iya Konawa da kuma tarwatsa birni mafi girma a duniyar yau. Sanadiyyar wannan gamammiyar tasiri da wannan makami ya mallaka tasa ake masa lakabi da makamin kare-dangi, ko kuma weapon of mass destruction, a harshen Turanci.

A tarihin duniya sau biyu kadai aka taba amfani da wannan makami don kai hari tsakanin wata kasa da wata kasa. Hakan ya faru ne lokacin yakin duniya na biyu, lokacin da kasar Amurka ta jefa wa kasar Jafan wani makaminta na nukilya mai dauke da nau’in makamashin yuraniyon, mai suna “Little Boy”, a babban birnin kasar Jafan na wancan lokaci, watau birnin Hiroshima. Wannan ya faru ne ranar 6 ga watan Agusta, shekarar 1945. Kwanaki uku da jefa wannan makami, sai Amurka ta sake dosan birni na biyu a girma, watau birnin Nagasaki, ta ajiye wa mutanen birnin wani makamin nukiliyanta mai dauke da makamashin fulutoniyon, mai suna “Fat Man”. Wannan ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu dari da ashirin nan take, tare da mutuwar wasu dubunnai akai-akai, sanadiyyar tururin haske mai dauke da guba da ke yawo a muhalli da sararin samaniyan biranen biyu. Kawo yanzu, akwai kasashe a kalla takwas, wadanda aka tabbatar da suna da wannan makami na nukiliya a duniya, sanadiyyar gwaji da suka yi kowa ya gani don tabbaci. Wadannan kasashe kuwa sune: Amurka, da Rasha, da Burtaniya, da Faransa, da Sin, da Indiya, da Pakistan, da kuma Koriya ta Arewa.

A yanzu akwai nau’ukan makamin nukiliya iri biyu, shahararru, wadanda dukkan wasu nau’uka suka dogara dasu. Nau’i na farko shine nau’in da ke dauke da makamashin madda mai karfi, masu tarwatsa juna ta hanyar warwatsuwar da suke yi yayin da aka harba su ta hanyar makamin da suke dauke cikinsa. Akan jejjera wadannan makamai masu gaggawar tarwatsewa ne waje daya, cikin kwanso ko makami guda kenan, sannan a harba su zuwa inda ake hari. Wannan tsari tsohon yayi kenan, kuma shi ake kira the gun method, domin akan harba makamin ne kamar yadda ake harba harsashi da ke cikin bindiga. Ko kuma, a daya bangaren, a jera makamai masu dauke da makamashin fulutoniyona wuri daya, cikin kwanso daya, da zarar an harba su, sai su harhade da juna, sannan su fashe. Wannan tsari shi ake kira the implosion method. Kuma su suka kunshi nau’in farko na makamin nukiliya mai suna Atomic Bomb, ko kuma A-Bomba takaice. Irin wannan nau’in ne kasar Amurka ta ajiye wa mutanen Jafan a manyan biranensu, lokacin yakin duniya na biyu, kamar yadda bayanai suka gabata a sama. Sai nau’i na biyu kuma, wanda ke haifar da makamashin guba mai dimbin yawa sanadiyyar hadewar sinadaran madda masu tarwatsewa irin wanda ke dauke cikin nau’in farko, da kuma wasu sinadaran madda masu hadewa kafin su tarwatse. Yadda ake kera wannan nau’in shine, za a shigar da sinadaran madda masu tarwatsewa cikin ma’adana daya mai dauke da makamashin tururin haske, a gefensu kuma a jejjera sinadaran makamashi masu gamewa da juna lokacin fashewarsu (irin su tritium da kuma deuterium, ko kuma lithium denteride), duk cikin kwanso ko ma’adana guda. Da zarar an jefa wannan makami a wurin da ake hari, sai wadancan sinadarai masu saurin tarwatsewa su tarwatse cikin ma’adanar. Tarwatsewarsu ke haifar da haske mai tsanani nau’in Gamma-ray da kuma X-ray, nan take sai wannan haske ya narka sinadaran lithium denteride, ya tafasa su matukar tafasawa. Suna gama tafasuwa sai kawai su haifar da sinadarai nau’in neutron, masu gamewa da makamashin yuraniyon don haddasa fashewa da kara mai tsanani. Wannan nau’i kuma shi ake kira Hydrogen Bomb,ko H-Bomb, ko Fusion Bomb, ko kumaThermonuclear Bomb, a turance. Kuma shi ne har wa yau Hausawa ke kira “makami mai guba”!

Asali da Bunkasar Makamin Nukiliya a Duniya

Wannan makami mai matukar tasiri wajen darkake rayuka da muhallin dan Adam ya samo asali ne shekaru kusan tamanin da suka gabata, lokacin da Hukumar Gwamnatin Amurka ta samo wasu kwararru kan makamashin nukiliya daga kasashen Jamus da Ingila da kuma Kanada. Wannan ya faru ne bayan yakin duniya na daya, lokacin da Hukumar Nazi da ke kasar Jamus ta aikata ta’addanci mafi girma kan wasu kasashe da kabilu irinsu Yahudawa da sauransu. Wannan tasa gwamnatin Amurka ta fara jin cewa zaman lafiyarta da kuma burinta wajen ci gaba da neman hanyoyin mallake duniya na fuskantar kalubale mafi girma. Don haka ta samo wadannan kwararru a boye, wajajen shekarun 1930s, don tsarawa da kuma kera mata makamin nukiliyarta ta farko, wanda kuma su ne tayi amfani da su kan kasar Jafan lokacin yakin duniya na biyu. Wadannan makamai ta kera su a wani tsari mai suna The Manhattan Project, ta kuma yi gwajin makaman nukilyarta na farko ne a watan Yuli na shekarar 1945, a wani gari mai sunaAlamogordo da ke New Mexico, a can Amurka. Hakan ya faru ne wata guda kafinta kai hari kasar Jafan. Daga nan sai kasar Hadaddiyar Daular Sobiet, watau kasar Rasha kenan a yanzu. Ta kuma samo dabarunta ne daga wasu ‘yan leken asiri da ta tura kasar Amurka suka sato fasahar tsarawa da kuma kera wannan makami. Kasar ta gama kera nata makaman ne a karon farko, cikin shekarar 1949, lokacin da tayi nata gwajin a fili kowa ya gani. Wannan ya faru ne bayan shekaru hudu da gama yakin duniya na biyu.

Da aka shiga shekarar 1950 zuwa shekarar 1960s, sai tsarin ginawa da kuma tsara wannan makami ya fara sauyawa. Makamin nukiliya da kasashen biyu suka fara kerawa shine nau’in farko cikin nau’ukan nukiliya biyu da bayanansu suka gabata a sama, watau nau’in Atomic Bomb. Ana shiga shekarar 1950 sai suka shiga tseren kera wasu sabbin nau’ukan wannan makami. A lokacin ne aka fara kera nau’in Hydrogen Bomb ko Fusion Bomb. A wajajen shekarar 1955 kuma aka kera hanyoyi dabam-dabam da ake amfani dasu wajen jefawa ko harba wannan makami. Shahararren makamin da suka kera shine roket, wanda ke sawwake daukan makamin nukilya cikin kwansonsa, ta hanyar roket din, don adana shi ko jefa shi a gari ko kasar da ake son aika mata. Hanyar farko wacce kasar Amurka tayi amfani da ita wajen darkake kasar Jafan lokacin yakin duniya na biyu ita ce ta yin amfani da jirgi mai dauke da makamin don jefawa a inda ake son jefawa, watau Airborne. Amma a wannan lokaci sai aka fara kirkirar makamin roket a matsayin makami na musamman don aikawa da shi, wanda shi ya fi tsananin sauri da dacewa wajen isarwa. Har wa yau, wannan hanya ce tafi karancin hasarar rayuka ko jirage ta bangaren kasa mai aikawa, ko da wacce aka aika mata da mukabulanci makamin.Saita shi kawai za a yi, a harba, ya rage wa kasar da aka jefo mata; idan tana da roket mai iya darkake wannan makami shikenan. In kuma bata dashi, sai Allah Sarki.

Wadannan kasashe biyu na samun wannan makami sai duniya ta sake shiga halin zaman dardar; kowacce nai wa ‘yar uwarta kallon hadarin kaji. Idan kasar Amurka tayi gwaji, sai ita ma kasar Rasha tayi nata gwajin. Ya zama kowacce na takama da nata makamin. Daga nan sai kasar Ingila ta shiga layi ita ma; ta mallaki nata makamin na nukiliya ta hanyar samun taimako daga kasar Amurka, babbar yaya kenan! Tana samun nata, sai kasar Faransa ita ma ta mallaki wannan makamin. Duk ta hanyar kasar Amurka suka samu. Domin a lokacin an shiga zamanin yakin cacar-baki, inda kasashen duniya suka rabu uku; da masu goyon bayan kasar Amurka (irinsu Ingila da Faransa da sauran kasashen Turai), da masu goyon bayan kasar Rasha (irinsu kasar Koriya ta Arewa da Sin da sauransu), sai kuma ‘Yan Ba -Ruwanmu.Don haka sai Amurka ta ci gaba da taimaka wa nata bangaren, ita kuma Rasha da ganin haka, sai ta koya. Kasar Faransa na samun nata, sai ga kasar Sin ita ma ta mallaki nata makamin na nukiliya. Wadannan kasashe su ake kiraThe Nuclear Club a duniya kuma daga kan su aka fara nazarin tasirin kowace kasa ta mallaki wannan makami a duniya, don haka sai aka fara neman hanyoyin magance yaduwarsa a duniya ta hanyar wasu yarjejeniyoyi da mai karatu zai samu bayaninsu nan gaba.

Daidai lokacin da aka kawo karshen yakin cacar-baki tsakanin kasar Amurka da Jumhoriyar Sobiet, sanadiyyar rushewar wannan jumhoriyar da kuma samuwar kasar Rasha ta yanzu, sai kasashen biyu (watau Amurka da Rasha) suka yi wa kawunansu karatun ta-natsu; inda suka kulla yarjejeniyar tsayar da habaka rumbunan makaman nukiliyarsu. Wannan ke nufin daga wancan lokaci, za su daina kera wasu sabbin makamai, da kuma ci gaba da adana wadanda suka mallaka kafin nan, don tsaron kasa. A wannan lokaci har wa yau, kusan dukkan makaman nukiliya da tsohuwar Jumhoriyar Sobiet ta mallaka suka koma hannun kasar Rasha, in ka kebe wasu kadan da aka rarraba wa wasu kasashe irinsu Yukiren da sauransu. Wannan yarjejeniya da kasashen Amurka da Rasha suka kulla ta sha bamban da wacce Majalisar Dinkin Duniya ta kafa. Wannan yarjejeniya ce a tsakaninsu, kuma sun yi hakan ne (a cewarsu), don rage zaman dar-dar da duniya ta shiga lokacin yakin cacar-baki.

Ana kara wasu ‘yan shekaru kuma, sai ga kasar Indiya ita ma ta mallaki nata makaman na nukilya. An kuma fahimci hakan ne ta hanyar gwajin makaman da tayi, wanda hakan ce hanya mafi tabbaci wajen nuna wa duniya cewa ita ma ta mallaki nata makaman, ayi hankali da ita. Ga dukkan alamu, kasar Indiya ta samu nata fasahar ne daga kasar Amurka, sabanin kasar Sin da ake tunanin daga kasar Rasha ta samu. Kamar yadda kowa ya sani, ba a ga-maciji tsakanin kasar Indiya da kasar Pakistan, watau makwabciyarta. Don haka sai kasar Pakistan ta dauki wannan a matsayin hannunka-mai-sanda ne makwabciyarta ke mata. Don haka, ana shiga shekarar 1998, sai ita ma kasar Pakistan tai nata gwajin, don nuna wa duniya (musamman ma kasar Indiya) cewa ita ma fa ta kawo! Daidai lokacin da kasar Pakistan tayi wannan gwaji, sauran kasashe sunyi ta korafi, musamman ma kasashen Turai da Amurka. To ita kuma daga ina ta samo nata fasahar? Zamu yi bayani nan gaba in Allah Ya yarda.

Wannan gwaji da kasar Pakistan tayi a shekarar 1998 ya kawo adadin kasashe masu mallakan makamin nukiliya zuwa bakwai.Daga nan dai Majalisar Dinkin Duniya, karkashin Cibiyar Makamashin Nukiliya ta Duniya, watau International Atomic Energy Agency (IAEA), wacce Mohammad El-Baradai ke shugabanta, taci gaba da karfafa kudirin ragewa da kuma hana yaduwar makamin a duniya, don samun lumana. Ana cikin haka sai aka fara samun rade-radin cewa kasar Koriya ta Arewa na shirya makamin nukiliya da ma wasu mizail masu cin dogon zango. Wannan tasa sauran kasashen yamma irin su Turai da Amurka, suka sa mata ido. Cikin shekarar 2006, sai Koriya ta Arewa ta yi nata gwajin, wanda ta gudanar ta karkashin kasa da cikin teku. Da farko wasu kasashen basu gasgata wannan ikirari nata ba, sai da wani hukumar tsaron Amurka ta yi nazarin tsarin hayakin da gwajin ya haifar, wanda ta dauko daga na’urorin hangen-nesa da ta kafa cikin teku, sannan ta tabbatar da cewa lallai abinda wannan kasa ta harba makamin nukiliya ne.Hakan ya cika adadin kasashen zuwa takwas, wadanda suka fito fili, suka nuna wa jama’a ko duniya, cewa lallai sun mallaki wannan makami.

Akwai wasu kasashe kuma wadanda ko dai sun ki fitowa fili su nuna wa duniya cewa sun mallaki wannan makami, duk cikakkiyar tabbaci da ake dashi kan sun mallaka, irin su kasar Isra’ila. Ko kuma wadanda zarginsu kawai ake cewa sun mallaka, amma babu tabbaci. Watakil saboda siyasar duniya.Kamar kasar Isra’ila misali, wacce ta ki fitowa fili ta nuna wa duniya cewa ta mallaki wannan makami, amma sauran kasashen duniya, hatta kasar Amurka, suna da tabbacin cewa kasar Isra’ila ta mallaki wannan makami tun wajajen shekarar 1986, amma gwamnatin Amurka bata fitowa fili tayi magana wanda ya shafi hani ko goyon baya ba. Sai dai akwai rahotanni da wasu jaridun Ingila da na Amurka suka bayar, da ke nuna cewa kasar Isra’ila ta mallaki a kalla makamin nukiliya kusan dari biyu. Bayan haka, a wannan shekarar tsohon shugaban kasar Amurka watau Jimmy Carter, ya gaya wa ‘yan jaridu cewa kasar Isra’ila ta mallaki wannan makami, amma hukumomi a Tel Aviv sun kasa fitowa fili su tabbatar ko karyata ire-iren wadannan rahotanni. Wannan ke nuna cewa akwai kamshin gaskiya a cikinsu. Sai kuma kasar Iran, wacce ake ta kai ruwa rana da ita kan cewa ta mallaki wannan makami ko kuma, a kalla, tana shirin mallakan wannan. Duk da cewa jami’an Cibiyan Binciken Makamin Nukilya ta Duniya watau IAEA, sun kai ziyara kasar, suka kuma tabbatar da cewa har yanzu babu wasu alamu da ke nuna cewa Iran ta mallaka ko kuma tana shirin kerawa, sauran kasashen Turai da Amurka basu yarda ba. Kasa ta karshe da ake ta rade-radin cewa tana shirin kera wannan makami ita ce kasar Siriya, wacce cikin shekarar 2007 kasar Isra’ila ta kai hari kan wani gini da ke kasar, cewa hukumar Siriya ta gina shi ne don fara shirinta na makamin nukiliya. Watanni biyu da suka gabata Hukumar IAEA ta tura jami’anta zuwa kasar Siriya don yin nazarin wannan gini da kasar Isra’ila ta darkake, don tabbatar da wannan zargi ko rashinsa.

Har wa yau, akwai wasu kasashe da suka fara shirin mallakan wannan makami, amma daga baya, ko dai saboda siyasar duniya ko kuma tsoron fushin kasashen Turai, suka bata shirin, tare da wargaza cibiyar da suka tanada a farko. Wadannan kasashe sun hada da kasar Libya, wacce ta bata nata shirin sanadiyyar surutun kasashen Turai. Tai haka ne don neman yardarsu, musamman da suka mata alkawarin bata tallafi don habaka makamashin lantarki da tace shine sanadiyyar da tasa ta fara wancan shiri.Shekaru kusan hudu da bata wannan shiri nata, bana tunanin sun cika mata alkawarin da suka dauka na bata tallafin kudi don habaka makamashin lantarkin da suka yi alkawari. Haka kasar Afirka ta Kudu ita ma ta fara wannan shiri na mallakan makaman nukiliya, amma sai ta wargaza, ba tare da ta bayar da wasu dalilai a fayyace ba.

Munanan Tasirin Makamin Nukilya

Makamin nukiliya, kamar yadda bayanai suka gabata a sama, na tattare ne da sinadaran kimiyya masu matukar illa ga rayuwa, musamman lokacin fashewar makamanin a wani wuri da aka harba ko jefa shi. Wannan ke wajabtar da samuwar illoli da dama ga rayuka da muhallin da makamin ya fashe. Muhalli ya shafi iskar da ake shaka a bigiren, da duwatsu ko tsaunukan da ke wannan muhalli da kuma teku ko koguna ko rafuka. Duk idan makamin ya fashe, zai shafe su mummunar shafa, tare da yada illolinsa ga duk wani abinda ya ta’allaka dasu; dabba ce mai rai ko wani abu dabam.

Da zarar an harba ko jefa makamin nukiliya a wani wuri, gari ne ko dajin Allah ta’ala, akwai abubuwa guda hudu da ke haddasuwa da zarar makamin ya fashe. Abu na farko shine kara mai tsananin firgitarwa, watau Blast a turance. Wannan kara mai tsananin firgitarwa shi ya kumshi kashi arba’in zuwa hamsin (40% – 50%) na bala’in da ke tattare da wannan makami mai narkar da rayuwa da muhalli. Har wa yau, yawa ko karfin wannan kara mai firgitarwa ya ta’allaka ne da yanayin makamin wajen kerawa. Makamin da ke cike da sinadaran makamashin nukiliya mai dimbin yawa yafi haifar da kara mafi girma da firgitarwa. Babban abinda ke haddasa wannan kara mai firgitarwa yayin fashewar makamin nukiliya su ne wasu dimbin makamashin sinadaran kimiyya masu dauke da maddar kimiyya masu tsananin hadari ga rayuwa da muhalli. Idan fashewa ya auku, zai haifar da wannan kara, wanda ke kumshe da iska mai bala’in tunkudowa don raunana dukkan wani abinda ta riska, tare da tarwatsa shi nan take babu kakkautawa. Wannan kara mai dauke da wannan iska mai bala’in tunkuda na haddasuwa ne cikin ‘yan dakiku (seconds), amma tasirinsu wajen tarwatsa muhalli da abinda suka darkake, ya zarce na dukkan wata mahaukaciyar guguwa mai dauke da iska (hurricane) da aka taba samu a duniya.An kiyasta cewa karfin wannan kara mai firgitarwa na iya kwantar da dukkan gidajen da ke bigiren da fashewar ta auku. Haka idan akwai hanyar dogo (jirgin kasa) a wajen, karar na iya daukan taragon jirgin ta jefar dashi wata duniya dabam.

Abu na biyu cikin abubuwan da fashewar makamin nukiliya ke haifarwa shine wani haske mai dauke da tururin guba ko sinadaran kimiyya masu illa ga muhalli da rayuwa.Wannan shi ake kira Thermal Radiation a turance, kuma yana fitowa ne da zarar wancan kara mai firgitarwa ya haifar da makamashin maddar kimiyya zuwa muhalli, wanda ke dabaibaye dukkan ilahirin wuri ko bigiren da fashewar ta auku cikin kasa da dakika guda. Wannan nau’in makamashin haske mai dumi da ake kira Thermal Radiation shine ya kumshi kashi talatin zuwa hamsin (30% – 50%) na makamashin da fashewar makamin nukiliya ke haifarwa. Kuma wannan tururin haske ya kumshi nau’ukan haske ne guda uku; na farko shine asalin haske irin na rana da ido ke iya jure ganinsa, wanda muke dashi a nan duniya kenan (watau Visible Light), sai kuma nau’in hasken da ido baya iya jure kallonsa, saboda gundarin haske ne mai cike da makamashi mai dimbin yawa (watau Ultraviolet Light), na karshe kuma shine nau’in haske mai dauke da makamashin Infra-red, watau hasken da ke kasa da ganin dan Adam, amma yana nan kuma yana da tasiri matuka ga muhallinsa da kuma jikinsa. Wadannan nau’ukan haske na cikakken tasiri wajen haddasa makantar wucin-gadi (na tsawon mintuna arba’in), ko tabbatacciyar makanta.Hakan ya danganta da kusancin mai idon da kuma wajen da aka samu fashewar makamin ne. Domin haske ne da ke shiga jiki ko duk abinda yayi karo dashi, tare da mannewa ko tabbata a jikin, bayan tasirin kuna mai tsanani da ya mallaka. Bayan dukkan wannan, tururin hasken Thermal na iya gurbata dukkan iskar da ake shaka da zarar ya fito, tare da haddasa maganadisun lantarki cikin iskar (Electromagnetic Shockwave), mai cikakken tasiri ga dukkan wani jiki, kamar yadda mayen-karfe (magnet) yake da sauran karafa!Da iskar da ke muhallin, da rafi ko kogi ko tekun da ke muhallin duk zai gurbata su. Kai hatta dutse ko wani tsauni dake wannan wuri yana iya samun nasa rabon. Idan ya samu damar saduwa da jikin dan Adam, ya kan raunana dukkan gabobinsa, ya haifar da mummunar illa ga kasusuwa da bargonsa, sannan ya karya wa jijiyoyinsa dukkan lagonsu, bayan haka, yabi mabudan hanji ko tumbi, da huhu da kuma gangar kunne, duk ya bata su ta hanyar rubar da su nan take! Abu na karshe da wannan tururin haske ya mallaka shine haddasa gagarumar gobara a muhallin da fashewar ta auku.

Abu na uku da ke haifuwa sanadiyyar fashewar makamin nukiliya shine tururin hayaki mai haifar da sinadaran kimiyya nau’in ayon, ko kuma ionization a turance. Wannan tururin haske aikinsa shine ya haifar da sinadaran madda masu tattare da maganadisun lantarki (Electromagnetism), masu taimaka wa tururin hasken Thermal da bayaninsa ya gabata, don gurbata yanayin gaba daya, da hana dukkan wani abin halitta sararawa. Wannan nau’in tururin haske na ayon shine kashi biyar (5%) na makamashin da makamin nukiliya ke fitarwa da zarar ya fashe. Wadannan nau’ukan tururi guda biyu, da zarar sun watsu cikin muhalli sanadiyyar fashewa da aka samu na makamashin nukiliya a wurin, to garin baya iya zaunuwa har abada. Wannan shine abinda ya faru da mutanen birnin Pripyat da ke kasar Yukiren (Ukraine), lokacin da wata masana’anta ko cibiyar nukiliya ta fashe, dole suka bar garin, don bazai zaunu ba. Saboda dukkan iska da ake shaka, da ruwa da ake sha da kuma muhallin shi kansa, duk sun gurbace matukar gurbacewa; wata halitta mai rai bata iya jure zaman wurin, balle ta amfana da abinda ke muhallin wajen gaba daya. Dole garin, duk da girma da kuma kayan alatun da ke cikinsa, ya zama fako, kowa ya gudu. Ire-iren wadannan garuruwa da ke samun kansu cikin wannan hali ana kiransu Nuclear Ghost Town a turance. Nau’in abinda ke samuwa daga fashewar makamin nukiliya na karshe shine hayaki mai dauke da haske, wanda ke tudadowa don mamaye ilahirin muhalli ko bigiren da fashewar ta auku. Wannan hayaki, wanda dan Adam na iya ganinsa, yana fitowa ne tare da masifaffen karar fashewar makamin, a matsayin wata gagarumar da’ira ta hayaki, wacce ke haurawa sama don yada dukkan sinadaran tururin hasken da bayaninsu ya gabata a baya. Da zarar wannan hayaki yayi ziri zuwa sama, sai ya warware yayi lema, don tarwatsawa da yada wadannan sinadaran guba, wadanda ke gurbata muhalli gaba daya. Wannan tarin hayaki shine ke daukan kashi biyar zuwa goma (5% – 10%) na yawan makamashin da makamin nukiliya ke fitarwa yayin fashewarsa. To me ye kimar hasarar da ke iya shafan rayuka ko ababen da ke kusa da wajen wannan fashewa?

Duk lokacin makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb ya fashe a wuri, duk wani abin halitta – ko gida ko dutse ko tsauni ko wani teku – da ke kusa da wurin fashewar da gwargwadon nisan mil guda, zai hallaka gaba daya. Babu abinda za a samu mai amfani tattare dashi.Idan kuma nau’in Hydrogen Bomb ne, duk abinda ke gwargwadon mil biyar ko nisan kilomita takwas zai hallaka nan take. Domin Hydrogen Bomb yafi Atomic Bomb masifa wajen hasarar rayuka da muhalli. Bayan nan, idan kuma nisan da ke tsakanin wata halitta ko gine-gine ya kai mil daya da digo biyu, ko gwargwadon kilomita biyu kenan, to zai samu mummunar illa wanda zai sa a gwammace rasa shi ma gaba daya. Idan kuwa nau’in Hydrogen Bomb ne, duk wanda ke iya nisan kilomita bakwai da fashewar na iya samun wannan mummunan illa. Idan, a daya bangaren kuma, fashewar ta uku a nisan kilomita uku ne, to duk wanda ke kusa da wajen iya takin wannan nisa na samun illa mummana wacce bata kai mutu-kwakwai-rai-kwakwai ba. Irin wannan illar na iya samun wanda ke nisan kilomita goma shabiyar tsakaninsa da fashewar Hydrogen Bomb. A karshe, halitta na iya samun takaitattun raunuka ko ‘yar karamar dameji, idan gine-gine ne, muddin aka samu tazarar kilomita biyar tsakaninta da wajen fashewar makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb, ko kuma nisan kilomita ashirin da bakwai idan nau’in Hydrogen Bomb ne. Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin bala’i ko masifar da ke dauke cikin makamin nukiliya. Kuma duk da yake kusan kowace kasa na burin kera wannan makami, amma Majalisar Dinkin Duniya tace kowa ya mayar da wukarsa cikin kube, ta haramta kerawa balle yada wannan makami.

Dokar Hana Yaduwar Makamin Nukiliya a Duniya

Bayan yakin duniya na biyu, da kuma abinda ya biyo bayan yakin na cacan-baki tsakanin kasar Amurka da Rasha, wanda sanadiyyar hakan suka shiga rige-rigen kerawa da kuma taskance dukkan nau’in wannan makami mai matukar hadari, Majalisar Dinkin Duniya bata samu natsuwa ba da wannan sabon salo.Wannan tasa nan take ta kafa hukuma ta musamman, wacce aka dora wa alhakin lura da yaduwar wannan makami a ko ina yake a duniya. Wannan hukuma, mai sunaInternational Atomic Energy Agency (IAEA) – Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya – an kafa ta ne cikin shekarar 1957.Babban kalubalen da wannan hukuma ta fara fuskanta shine kaddamar da bincike na musamman don gano yawa da kuma nau’ukan da kowace kasa ta mallaka, tsakanin kasar Amurka da Rasha.

Majalisar Dinkin Duniya tace kafa wannan hukuma ya zama dole, idan aka yi la’akari da munanan tasirin wannan makami wajen salwantar da rayuka da kuma muhalli. Babban misali shine abinda ya faru ga kasar Jafan lokacin yakin duniya na biyu; lokacin da kasar Amurka tai mata kaca-kaca – babban abinda ya durkusar da kasar gaba daya a wancan lokaci. Dalili na biyu kuma shine, ta la’akari da sabon nau’in wannan makami, watau Hydrogen Bomb, wanda ya shallake nau’in Atomic Bomb wajen barna da yada munanan tasirinsa ga muhalli, Majalisar Dinkin Duniya tace muddin aka sake wasu kasashe biyu (musamman Rasha da Amurka) suka barke da yaki, to duniyar ma ana ganin baza ta zaunu ba, domin tasirin wannan makami na iya darkake dukkan kasashen da ke makwabtaka da su, har abin ya shafi kowace kasa. A karo na karshe, hukumar ta kara kaimi wajen aikinta musamman tun bayan harin da aka kai wa kasar Amurka, wanda ya darkake babban cibiyar kasuwancin duniya, cikin shekarar 2001. Ta ce hakan ya zama dole, don tabbatar da cewa kungiyoyi irin su Al-Qa’ida basu mallaki wannan makami ba a hannunsu. Domin hakan na iya zama babban hadari ga duniya, a cewar hukumar. Don a yayin da ake iya yin himma wajen kare kai daga harin da wata kasa ke iya kawowa, su ire-iren wadannan kungiyoyi ba a ganinsu, babu wanda ya san inda suke, ba wanda ya san ta jihar da zasu jefo – a wani lokaci, da wani irin nau’i zasu yi amfani? Haka idan suka kawo wa wata kasa hari, ba yadda za a yi kasar ta iya ramawa, domin basu da kasa tasu ta kansu, kuma basu takaita da wani bigire ba! Wadannan, inji hukumar, na cikin manyan dalilan da suka sa aikinta ke da matukar muhimmanci, musamman a wannan zamani da muke ciki.

Manyan aiyukan wannan hukuma dai su ne, hana yaduwar wannan makami na nukiliya gaba daya musamman ga kasashen da basu mallaki makamin ko ba, da kuma tabbatar da cewa wadanda suka mallaka tun farkon lamari, sun bata nasu makaman gaba daya. Babban magana! Haka kuma, Hukumar na da hakkin shiga dukkan kasar da ta rattafa hannunta kan wannan yarjejeniya, don aiwatar da bincike kan wannan makami.Babu ruwanta da kasashen da basu sanya hannu ba kan yarjejeniyar. Na biyu kuma shine lura da kuma habaka yaduwar makamashin nukiliya a duniya (bayani na nan tafe kan wannan). Domin sinadaran kimiyyar da ake sana’anta makamin nukiliya dasu ba wai makami kadai ake iya yi dasu ba, a a, su kansu makamashi ne na musamman wajen samar da wutar lantarki. To, aikin wannan hukuma shine ta taimaka wajen samar da wannan makamashi ga dukkan kasar da ke so.Wadannan, su ne manyan aiyukan wannan hukuma. Ana kafa wannan kungiya, sai kasar Amurka da Rasha suka sasanta a tsakaninsu, inda suka kulla yarjejeniyar cewa baza su kara kera wasu makaman ba, kuma zasu ci gaba da kokarin ganin cewa sun rage yawan makamin da suka mallaka. Haka nan, sun yi yarjejeniya cewa duk wata kasa da zata yi gwajin makaminta na nukiliya, to dole ne tayi shi ta karkashin kasa, ba a doron duniyarmu ba. Sun yi wannan yarjejeniya ne cikin shekarar 1963, kuma ita ce yarjejeniyar da suke kira Partial Test Ban Treaty (PTB). Manufar wannan shine don hana gurbata muhalli, sanadiyyar tasirin sinadaran wannan makami na nukiliya. Ana shiga shekarar 1970, sai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta fito da yarjejeniyar hana yaduwar makamin nukiliya a duniya gaba daya.Wannan yarjejeniya ita ake kira Nuclear Non-Proliferation Treaty (NPT). Hana yaduwa na nufin hana kerawa da kuma yada shi ko raba shi ga wasu kasashe.Amma har zuwa shekarar 1995, dokar hana gwajin makami a doron kasa ce ke aiki kadai. Duk wacce ke son yin gwaji, dole ne ta yi gwajin cikin karkashin kasa.Ana shiga shekarar 1996 sai wannan hukuma ta haramta gwajin makamin nukiliya ma gaba daya. Domin hakan, a cewarta, ita ce hanya mafi sauki wajen hana yaduwar makamin a duniya; tunda sai an yi gwaji ake gane tasirin makamin.Zuwa yanzu akwai kasashe dari da talatin da suka rattafa hannunsu kan wannan yarjejeniya ta hana yaduwar wannan makami a duniya.

Hukumar na da hedikwata a birnin Biyenna da ke kasar Awstiriya, cikin Turari kenan. Ya zuwa yanzu, ta bata ko kuma taimaka wajen bata cibiyoyin bincike da kera makamin nukiya a duniya a kasashe dabam-daban. Wasu cikin kasashen sun hada da kasar Afirka ta Kudu, da kasar Libiya da kasar Iraki, bayan yakin Golf, don hana tsohon shugaba Saddam Hussein kera wannan makami, a cewar hukumar. A yanzu dai shugaban wannan hukuma shine Mohammad El-Baradai, wani masanin fasahar nukiliya a duniya, dan kasar Masar. Bayan ya shugabanci wannan hukuma sau biyu, a karo na uku kasar Amurka bata so ya zarce ba, saboda yaki yarda da rade-radin da take na cewa lallai sai an kai wa kasar Iraki hari don bata abinda ta kira kerawa da kuma taskance kamamin kare-dangi da tsohon shugaba Saddam Hussein ke yi, cikin shekarar 2003. El-Baradai bai goyi bayan wannan ikirari nata mara asali ba, wannan tasa kasar Amurka taki goyon bayansa.Amma a karshe dai ta lura cewa dukkan sauran kasashe na sam-barka da shugabancinsa, a dole ta goya masa baya ya zarce a matsayin shugaban wannan hukuma a karo na uku. Wannan ya faru ne cikin shekarar 2005. Ana sa ran saukarsa cikin shekarar 2010 kenan.

Har wa yau, wasu kasashe ko nahiyoyin duniya sun kulla yarjejeniyoyin hana yaduwar wannan makami a tsakaninsu, bayan yarjejeniyar asali da wannan hukuma ta assasa kenan. Ire-iren wadannan kasashe ko nahiyoyi ana kiransu Nuclear Free Zone a turance. Daga cikinsu akwai wanda kasashen nahiyar Amurka (Latin America) suka kulla a tsakaninsu, cikin shekarar 1967. Wannan yarjejeniya suna kiran ta Tlatelolco Treaty,kuma ita ce ta haramta yada dukkan wani abu mai alaka da makamin nukiliya a wannan nahiya gaba daya. Sai kuma wacce kasashen Afirka suka kulla mai suna Treaty of Pelindaba, wacce ita ma ta hana, tare da haramta kerawa ko yada makamin nukiliya a tsakanin kasashen Afirka. An kulla wannan yarjejeniya ne cikin shekarar 1964. A shekarar 1996 kuma, sai babban kotun duniya da ke kasar Nedalan, watau International Court of Justice (ICJ), ta aiyana cewa yin amfani da makamin nukiliya wajen kerawa ko yada shi, ya saba wa dukkan dokokin Majalisar Duniya, da Babban Yarjejeniyar Janeba (The Geneva Convention), da Yarjejeniyar Heg da kuma manyan Dokokin Kare Hakkin Dan Adam (Universal Human Rights).

Kasashe Masu Karfin Nukiliya a Duniya

A yanzu akwai kasashe tara da aka tabbatar suna da wannan makami. Inda aka bambanta kawai shine, yawan makamin da kowace kasa ta mallaka.Wasu kasashen sun ki bayyana hakikanin abinda suka mallaka. Wasu ma sun ki yarda a aiwatar da bincike na musamman kan makaminsu. Wannan tasa sanin hakikanin abinda kowacce daga cikinsu ta mallaka a tantance, ke da wuya matuka. A halin yanzu zamu yi bayani filla-filla, kan kowacce daga cikinsu, da kuma kiyasin abinda ta mallaka, da lokacin da ta fara mallakarsa, da kuma lokacin da tayi gwaji da dai sauran bayanai masu alaka da hakan.

Kasar Amurka

Kamar yadda bayani ya gabata kan tarihi da asalin wannan makami, kasar Amurka

ce ta fara kera shi, tare da taimakon wasu kwararru kan harkar kimiyya daga kasashen Ingila da Kanada. Ta fara aikin ne a shekarar 1937, karkashin wani shiri da ta sanya wa suna ‘The Manhattan Project’, amma bata gama ba sai gab da yakin duniya na biyu. Daidai lokacin da take tunanin kera wannan makami, akwai rade-radin cewa Hukumar Nazi ta kasar Jamus na kokari kan haka. Sai kasar Amurka tayi gaggawa don tabbatar da cewa ta rigi kasar Jamus din. In yaso, idan ma yaki ne ya taso, to tana da makamin da Jamus bata dashi, ko kuma a kalla tana da abin kare kanta. Amma abin bakin ciki, wannan makami bai yi aiki a kan wadanda ake tunani ba, sai a kan ‘yan kasar Jafan, lokacin yaki na biyu. Amurka tayi gwajin farko ne a shekarar 1945, gwajin da ta sanya wa suna “Trinity”, kuma ita ce kasa daya tilo, wacce ta taba amfani da wannan makami don kai hari ga wata kasa a duniya gaba daya. Ta kai wannan hari ne da makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb, lokacin da ta darkake biranen Hiroshima da Nagasaki. Ita ce kuma kasa ta farko har wa yau, da ta fara kera makamin nukiliya nau’in Hydrogen Bomb, ta kuma gwada wannan makami da ta sa wa suna “Ivy Mike” ne a shekarar 1952. A shekarar 1954 kuma ta sake gwajin wani nau’in H-Bomb mai rai, wanda ta ma suna “Castle Bravo”. A halin yanzu kasar Amurka na da makamin nukiliya da adadinsu ya kai dubu biyar da dari biyar da talatin da biyar (5,535); guda dubu hudu da saba’in da biyar (4,075) masu rai ne, ana iya harba su da zarar bukatar hakan ta kama.

Kasar Rasha

Ita ce kasa ta biyu da ta mallaki wannan makami na nukiliya bayan kasar Amurka, ta kuma mallaki fasahar yin hakan ne ta hanyar tura kwararru kan kimiyyar makamai ta karkashin kasa, don sato ilimin wannan fasaha daga kasar Amurka.Tayi gwajin farko a shekarar 1947, da wani makami da ta sanya wa suna “RDS-1”.Babban abinda ya kara wa kasar Rasha kaimin mallakar wannan makami shine don taji dadin adawa da kasar Amurka lokacin da suka shiga shekarar yakin cacar-baki. Akwai tabbacin a kowane lokaci tana iya fuskantar kalubalen yaki daga kasar Amurka. Bayan haka, ita ce kasar Turai ta farko da ta fara mallaka tare da yin gwajin makamin nukiliya a dukkan ilahirin nahiyar turai. Ta kuma kera makamin nukiliya nau’in H-Bomb ita ma, cikin shekarar 1953, lokacin da tayi gwajin makamin mai suna “Joe-4”. Ta kuma zarce, don gwada wani makami mai cin miliyoyin zango a shekarar 1955, mai dauke da nau’in H-Bomb, mai suna “RDS-37”. Har wa yau, kasar Rasha ce ta taba gwada wani makamin bam, wanda babu wanda ya taba gwada irinsa a duniya, mai suna “Tsar Bomber”. Wannan makami na dauke ne da tan miliyon dari na makamashin nukiliya. Duk wannan, ita ma, tayi yi su ne a matsayin tauna aya, don tsakuwa taji tsoro. A halin yanzu kasar Rasha ta mallaki makamin nukiliya wanda adadinsa ya kai dubu goma sha shidda (16,000). Guda dubu biyar da dari takwas da talatin (5,830) masu rai ne, sauran kuma na kwance. Wannan ya sanya Rasha a matsayin kasar da ta zarce kowace kasa yawan makamin nukiliya a duniya.

Kasar Ingila

Ita ce kasa ta uku da mallakar wannan makami, kuma hanyar da ta bi wajen mallaka ba wani boyayye bane.Kasancewarta cikin kasashen da aka yi amfani da kwararrunsu wajen kirkirar wannan makami a Amurka, shi ya bata damar mallaka a shekarar 1952, lokacin da tayi gwajin farko da ta sanya wa suna ‘Hurricane’. Wannan gwaji, kasar Ingila bata yi shi a kasarta ba, kamar yadda sauran kasashen da suka gabace ta suka yi. Ta je kasar Austiraliya ne, cikin tsibirinMonte Bello, daidai wani wuri da yanzu ake kira Maralinga Tjarutja, don yin gwajin.Bayan tayi, an samu ambaliyar tururin haske mai guba (Radioactive Radiation),wanda ya shafi asalin kabilun da ke wannan bigire masu suna Aborigines. Don haka kasar Austiraliya tace bata yarda ba, sai da aka biya ta diyya kan haka. Ita ce kasa ta biyu a Turai da ta mallaki makamin, kuma babban abinda ya zaburar da ita shine don nuna wa kasar Rasha cewa ita ma tana nan; kasancewarta kawar Amurka. Kasar Ingila ta kera makamin nukiliyanta nau’in H-Bomb a shekarar 1957, kuma ta mallaki manyan jiragen ruwa masu karfin kai hari da makamin nukiliya a ko ina a duniya(watau Ballistic Missile), wajen guda hudu.A halin yanzu adadin makaminta na nukiliya sun kai dari biyu (200).

Kasar Faransa

Kasa ta hudu da mallakan wannan makami ita ce kasar Faransa, wacce hankalinta ya kasa kwanciya lokacin da ake ta hargowa tsakanin kasar Amurka da Rasha, kan tsibirin Suwiz (Suez Canal) da ke gab da ita. Don haka ta mallaki nata makamin cikin shekarar 1960, lokacin da tayi gwajinta na farko, kan wani makami mai suna “Gerboise Bleue”. Ta yi gwajin makamin nukiliyanta nau’in H-Bomb cikin shekarar 1968, karkashin wani shiri da ta kira “Operation Canopus”. Ita ma, kamar kasar Ingila, ta mallaki manyan jiragen ruwa masu karfin cilla makamin nukiliya daga teku zuwa kowace kasa ne a duniya.Har wa yau, tana da jiragen sama masu karfin jefowa ko diro da makamin nukiliya a matsakaicin zango (Medium Range Air-to-surface Missiles), masu suna Rafale Fighter-Bombers. Cikin Janairun shekarar 2006, shugaban kasa Jacques Chirac ya bayyana cewa, kasar Faransa a shirye take da ta kare kanta daga kowane irin hari ne da ya shafi makamin nukiliya a duniya. A halin yanzu adadin makaminta ya kai dari uku da hamsin (350).

Kasar Sin

Ita ce cikon ta biyar a jerin kasashen da ake kira The Nuclear Club. Su ne kasashen da suka mallaki makamin nukiliya tun kafin a kulla yarjejeniyar hana yaduwa balle kera makamin a duniya. Kasar Sin ta mallaki nata makamin ne a shekarar 1964, ta kuma yi gwajin farko wanda ta sanya wa suna “596’ ne cikin wannan shekara.Ita ce kasar Asiya ta farko da ta fara mallakan wannan makami, kuma ita ma tayi haka ne don a san da zamanta a wannan nahiya – musamman ganin yadda kasashe irinsu Amurka da Rasha ke ta fankama don mallakan wannan makami, a wancan lokaci. Kasar Sin ta kuma yi gwajin makamin nukiliya nau’in H-Bomb a shekarar 1967, daidai wani bigire mai sun Lop Nur. A halin yanzu kasar Sin ta mallaki makamin nukiliya guda dari da sittin (160), dari da talatin cikinsu masu rai ne, a farke suke!

Kasar Indiya

A farkon al’amari, duk kasashen duniya sun san kasar Indiya a matsayin kasa ce mai sarrafa makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki, wanda wannan na cikin abinda Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ke lura da bunkasa shi. Kasar Indiya ta fara mu’amala da fasahar Nukiliya ne tun wajajen shekarun 1970s, sanadiyyar samar da wutar lantarki da take yi ta amfani da makamashin sinadaran Nukiliya. Amma kuma, abin mamaki, taki ta sanya hannu kan yarjejeniyar hana kerawa da yada makamin nukiliya, kamar sauran kasashe, duk kuwa da dadewa da tayi tana amfana da makamashin, da kuma ganin cewa wannan shine abinda dama ake so, ba wai kera makamin ba.Ashe da biyu, wai an daki biri da rani. Cikin shekarar 1974 kasar tayi gwajin wani ‘halattaccen makamin nukiliya’, wanda mizani da tsarinsa bai kai sanannen makamin nukiliya ba. Ta sanya wa wannan makami suna ‘The Smiling Buddha’. Wannan abu da kasar Indiya tayi ya haddasa cece-kuce tsakanin kasashen duniya, na yadda tayi dabarar kera makamin nukiliya sanadiyyar amfani da makamashin da take yi. Sai a lokacin aka lura cewa, ashe bata sanya hannu kan yarjejeniyar hana kera wannan makami ba, balle a tuhume ta. Tayi dabara kenan! Alal hakika kasar Kanada tafi kowa bakin ciki kan abinda kasar Indiya tayi, domin ita ce ke sayar wa kasar da sinadarai tare da fasahar makamashin don samar da wutar lantarki. Babban abinda ya zaburar da ita, kamar sauran kasashe, shine ganin cewa kasashe irin su Sin da Rasha sun sanya ta a tsakiya. Don haka ita ma ta kama dahir.Cikin shekarar 1998 tayi wani kyakkyawan gwaji kan wani makamin nukilya mai rai, karkashin wani shiri mai suna ‘Operation Shakti’. Da tafiya tayi nisa, ya tabbata cewa kasashen Yamma sun yi na’am da wannan dabara da kasar Indiya tayi, don kasar Amurka ta kulla yarjejeniyoyi da ita cikin shekarar 2006. Wannan tasa masu lura da harkokin siyasar duniya ke ganin wata alama ce da ke nuna cewa an shigar da ita cikin kasashe masu hakkin mallakar makamin nukiliya na halal (Nuclear Club).Har wa yau, cikin shekarar ne dai Shugaban Amurka George W. Bush ya ambaci kasar Indiya a matsayin wata “Dattijiyar Kasa mai Karfin Nukiliya!”.Wadannan yarjejeniyoyi da aka kulla tsakanin Amurka da Indiya sun samu tabarrakin dukkan Majalisun kasar Amurka baki daya. A halin yanzu kasar Indiya na da makamin nukiliya da adadinsu ya kai dari da arba’in, kuma masu rai ne.

Kasar Pakistan

Kowa ya san yadda aka raba kasar Indiya gida biyu bayan samun ‘yancin kai, lokacin da kasar Pakistan ta samu nata bangare, kasancewar galibinsu Musulmi ne. Tun sannan suke ta fafatawa a tsakaninsu, musamman kan bodan Kishmeer da ke tsakaninsu. Don an rabu ne dutse a hannun riga. Don haka kasar Pakistan na jin makwabciyarta ta mallaki makamin nukiliya, sai ita ma ta sha alwashin lallai sai ta mallaka. Firanministan kasar Pakistan na wancan lokaci, Zulfiqar Ali Bhutto, ya fara wannan alwashi cikin shekarar 1965, cewa ‘muddin kasar Indiya ta mallaki makamin nukiliya, to mu ma sai mun mallaki namu; ko da kuwa hakan zai kai mu ga cin ciyawa ne (saboda talauci)’. Kamar kasar Indiya, ita ma Pakistan ta fara ne daga samar da makamashin wutar lantarki ta amfani da makamashin nukiliya. Cikin shekarar 1970 ta kafa cibiya kan makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki. Akwai alamun ta san abinda makwabciyarta ke yi a daidai wannan lokaci. Don cikin wadannan shekaru (1970s) ne ita ma ta fara hakilon samo fasaha iri-iri daga kasashen Yamma, don wannan aiki a boye. Wanda ke da alhakin wannan aiki kuwa shine Dakta Abdulqaadir Khan, wani kwararren injiniya kan kimiyyar karafa (Metallurgist). Yayi aiki a wata masana’antar makamashin nukiliya da ke kasar Nedalands a shekarar 1972, inda hukumomin kasar suka fara tuhumarsa da aikin leken asiri don satar fasahar makamin nukiliya a madadin kasarsa. To amma bayan shekaru biyu (1974), sai ya bar kasar, don dawowa gida Paskitan.Hukumar Nedalands ta so ta kai shi kotu kan wannan tuhuma da take masa, amma sai Hukumar Leken Asirin kasar Amurka, watau CIA, ta bata tabbacin cewa ba matsala, suna lura da jujjuyawarsa cikin abinda yake yi. Dawowarsa gida ke da wuya, sai shugaban Pakistan na wancan lokaci, watau Muhammad Zia’ul Haqq, ya bashi matsayin mai lura da wannan shiri na samar da makamin nukiliya ga kasar gaba daya. Yayi yawace-yawace zuwa wasu kasashe don wannan aiki. Akwai kuma tabbaci cewa kasar Sin ta taimaka wa Pakistan wajen wannan shiri. Wannan ya taimaka musu sosai, inda suka samu mataki na farko na wannan makami daidai shekarar 1980. Har zuwa wannan lokaci, kasar Pakistan bata rattafa hannu kan yarjejeniyar hana kera makamin nukiliya a duniya; ita ma ta kame, kamar yadda makwabciyarta tayi a farkon lamari. Har zuwa shekarar 1990, lokacin da kasar Amurka ta tabbatar wa duniya cewa lallai kasar Pakistan ta mallaki wannan makami, wanda hakan ya sa ta yanke dukkan wata alaka da ta shafi harkar soji da tattalin arzikin kasa a tsakaninsu. Don haka, kasar Indiya na kaddamar da gwajin da tayi cikin shekarar 1998, sai kasar Pakistan ta nuna wa duniya cewa ita ma fa ta kawo. Nan take ta kaddamar da nata gwajin na nukiliya, wanda tayi a saman wani tsauni da ke lardin Chagai. Ta kuma sanya wa wannan makami suna Chagai-1. A halin yanzu duk duniya ta sheda cewa kasar Pakistan ta mallaki wannan makami, kuma zuwa yanzu, tana da adadin makamin nukiliya masu rai, masu jiran ko-ta-kwana, guda sittin (60).

Kasar Koriya ta Arewa

Sabanin kasashen Indiya da Pakista, kasar Koriya ta Arewa mamba ce cikin kasashen da suka rattafa hannunsu kan yarjejeniyar hana yaduwar makamin nukiliya a duniya, amma da ta ga baza ta sha ba kan manufarta da ke boye, sai ta fice daga kaidin wannan yarjejeniya cikin shekarar 2003. Abinda ya haddasa hakan kuwa shine zarginta da kasar Amurka tayi, cewa lallai tana ci gaba da inganta makamashin Yuraniyon ta karkashin kasa, wanda hakan ya sha bamban da manufar samar da wutar lantarki. Ana shiga shekarar 2005 sai kasar ta ayyana cewa ta mallaki wannan makami na nukiliya.Amma kwararru kan harkar suka ki amincewa da wannan ikirari nata. Don haka sai ta gudanar da gwajinta na farko cikin shekarar 2006, sanadiyyar matsin-lamba da kasar Amurka ta ke mata ta karkashin kasa. Ta sanya wa wannan gwaji nata suna “The Beginning”. Da farko babu wanda ya yadda cewa gwajin makamin nukiliya ne, saboda makamashin da makamin ya fitar sanadiyyar gwajin bai kai na wadataccen makamin nukiliya ba. To amma daga baya, sai kwararru kan nukiliya da ke kasar Amurka suka tabbatar da cewa lallai makamin nukiliya ne, bayan sun yi nazarin hayakin da makamashin ya haifar lokacin gwajin, wanda na’urar tauraron dan Adam ta kasar ta dauko musu daga sararin samaniya. A yanzu kasar Koriya ta Arewa ta mallaki wannan makami har guda goma (10), ta kuma kaddamar da gwajinta na farko ne cikin teku.

Kasar Isra’ila

Na tabbata duk masu karatu zasu yarda idan nace kasar Isra’ila na cikin kasashen da ba kowa ya san halin da suke ciki ba, ta kusan dukkan bangarorin rayuwa kuwa.Wannan haka yake, kuma har zuwa yanzu, Hukumomi a birnin Tel Aviv sun ki fitowa su fadi matsayinsu kan rade-radin da ake ta yi cewa kasar ta mallaki makamin nukiliya tun wajajen shekarar 1979. Da farko dai, kasar Isra’ila ba mamba bace cikin yarjejeniyar hana kerawa da yada makamin nukiliya. Ma’ana bata rattafa hannunta kan wannan yarjejeniya ba, sam.Wannan ke nuna cewa ba da banza ba taki rattafawa. Na biyu, akwai rade-radin da ke nuna cewa tayi gwajin makamin nukiliyarta ne ta hadin gwiwa da kasar Afirka ta Kudu, wacce tuni ta wargaza nata shirin ba tare da matsin-lamba daga wata kasa ba. Wannan gwaji sun yi shi ne cikin shekarar 1979, kamar yadda ake ta rade-radi. Na uku, akwai shiri mai rikitarwa da kasar ta fara yi cikin shekarar 1960, kan abinda ya shafi mallakar makamin nukiliya. Amma da Yizthak Rabin yaje ziyarar aiki a matsayinsa na Ambasadan kasar Isra’ila zuwa Amurka, aka tambayeshi kan wannan shiri da kasarsa ke yi, sai yace “mallakar makamin kawai ba tare da gwaji ba, baya nuna cewa an mallake shi, sai an yi gwaji sannan hakan zai nuna ana da wannan makami”.Wannan kawai hargowa ce irin ta harshen diflomasiyya. Kuma galibin masu lura da harkokin siyasar duniya sun dauki wannan batu a matsayin tabbaci ne, duk da kwane-kwanen da yayi ta yi. Dalili na hudu da ke nuna lallai kasar Isra’ila ta mallaki wannan makami shine samuwar masana’anta ko cibiyar binciken nukiliya a garin Dinoma, wanda a farko hukumomin kasar suka karyata, suka ce masana’antar saka tufafi ce, ba ta nukiliya ba. Amma a karshe bayanai sun nuna ba haka bane, lokacin da wani kwararre kan harkar makamin nukiliya na kasar mai sunaMordechai Vanunu ya fasa kwai cikin shekarar 1986, inda ya tabbatar wa duniya cewa lallai kasarsa ta mallaki wannan makami, kuma shi ma ma’aikaci ne a wannan masana’anta. Jaridar The Sunday Times da ke kasar Ingila ce ta dauki wannan labaria shekarar 1986, kuma duk duniya ta karanta. Amma wani abin mamaki shine, Hukumar Isra’ila taki yin bayani kan haka, sai ma kama wannan bawan Allah tayi, ta yanke masa hukuncin zama gidan kaso na tsawon shekaru goma shatakwas, da sunan wai yaci amanar kasa.

A nasu bangaren, kwararrun masana kan fasahar nukiliya a Amurka da ke karkashin Kungiyar Masana Kimiyya ta kasar, watauFederation of American Scientists (FAS),sun tabbatar da manyan alamu da ke nuna cewa Isra’ila ta kera makamin nukiliya. Wannan kungiya ta samu wannan tabbaci ne daga hotunan da na’urar tauraron dan Adam na kasar Amurka yai ta daukowa daga sararin samaniya, mai nuna manyan motocin daukan mizail, wanda shine sanannen kwanson da galibi ake amfani dashi wajen harbawa ko jefa wannan makami, tare da wasu mazubai irin na diban makamai (Weapon Bunkers),a wasu wurare da ke nuna bigiren atisaye ne na wucin-gadi. A nasu kiyasin, sun nuna cewa kasar ta mallaki a kalla abinda ba ya kasa saba’in zuwa dari biyu (70 – 200), na makami mai rai. Ana cikin haka sai ga dalili na karshe, ranar 26 ga watan Mayu na wannan shekara, inda tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter ya tabbatar wa duniya a taron da yayi da ‘yan Jaridu a birnin Wales na kasar Ingila, cewa lallai kasar Isra’ila ta mallaki wannan makami na nukiliya. Ya kuma nuna cewa a halin yanzu, Isra’ila na da kawunan makami masu rai na nukiliya, guda dari da hamsin (150). Idan muka dubi dalilan da ke sama, da ikirarin da wasu masana suka ta yi, zamu ga cewa babu warwara tsakanin saba’in zuwa dari biyu, da kuma adadin dari da hamsin da Jimmy Carter ya bayar. Wanan shi ke nuna cewa kasar Isra’ila ce ta fara kawo makamin nukiliya a nahiyar Gabas-ta-tsakiya. Kuma har zuwa yanzu, babu wata kasa da ta mallaki wannan makami, in ka kawar da kasar Iran da ake ta kai ruwa rana da ita. Kai a zahiri ma dai kasar Iran bata riga ta mallaki wannan makami ko ba. Domin a iya binciken da hukumar leken asirin Amurka tayi shekaru hudu da suka gabata, ta nuna cewa ‘muddin kasar Iran taci gaba da inganta makamashin Yuraniyon kamar yadda take a yanzu (2003), tana iya samun mizanin da zai bata damar kera makamin nukiliya tsakanin shekarun 2010 – 2015.’ Wannan shine abinda hukumar ta fada. Kuma hatta Hukumar Lura da Makamin Nukiliya ta Duniya ta tabbatar da hakan, bayan ziyarar aiki da tayi ta kaiwa kasar, cikin shekarun baya. Me zai hana a kai irin w annan ziyara a kasar Isra’ila? Da an sha mamaki kuwa!

Rubutawa; Abdullah a shafin shi na blogger.

Share This Post
Have your say!
00

Customer Reviews

5
0%
4
0%
3
0%
2
0%
1
0%
0
0%

Leave a Reply

Thanks for submitting your comment!