Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da wani kudurin doka na kara harajin da ake biya kan wasu kayayyaki daga kashi 5 cikin 100 zuwa kashi 7.5 cikin 100 a ranar Alhamis.

Matakin dai ya janyo ce-ce ku-ce da dama a duk fadin kasar, inda wasu ke ganin cewa hakan zai kara yawan kudadden shiga ga kasar, wasu kuma na cewa hakan zai shafi rayuwar talakawa.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta aiwatar da kasafin kudinta na shekarar 2020 ne a kan kudin harajin kayayyaki, kan hakan ne ta yanke hukuncin kara yawan haraji.

Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari
Gwamnatin ta ce ta yi la’akkari da talakawa, saboda ta tsame wasu kayayyaki da harajin bai shafa ba kamar kayan koyarwa a makarantu da magunguna da kuma wasu kayayyakin abinci da ake amfani da su na yau da kullum.

Ga wasu daga cikin abubuwan da harajin bai shafa ba:

 1. NamaBurodi
 2. kifi da makamantansa
 3. Masara
 4. Shinkafa
 5. Fulawa
 6. Kwai
 7. Gero da
 8. Alkama
 9. Doya
 10. Dankalin Turawa da na Gida
 11. Ruwa
 12. Madara
 13. Gishiri

Shi dai shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya jadadda cewa wannan dokar ba wai an yi ta ba ne ba domin cutar da ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa gwamnati na son amfani da kudadden da za a samu ne domin kara habaka ababen more rayuwa.

SANARWA! GobirOnline.com na bukatar Karin ma’aikata (Voluntary), kwararru, ta fannin watsa Labarai, Tarihi, wasanni da Al’adu, Domin bunkasa ayukkan wannan shafin.

CONTACT US

We're not around right now. But you can send us an email and we'll get back to you, asap.

Sending

©2019 GobirOnline  all right received | Arewa-community | G. D. A.

or

Log in with your credentials

or    

Forgot your details?

or

Create Account