jerin jihohi 30 da ke cin moriyar shirin ciyar da dalibai

Fadar shugaban kasa ta saki jerin jihohi 30 da ke cin moriyar shirin ciyar da dalibai

Gwamnatin tarayya ta ce shirin ciyar da daliban makarantar firamare da abincin da aka noma a Najeriya ya mamaye jihohi 30 na kasar nan – Ta bayyana cewar yanzu haka shirin na ciyar da dalibai miliyan 9.2 a cikin dalibai miliyan 12 da shirin ke da niyyar ciyar wa a fadin Najeriya – Gwamnatin ta Buhari ta ce manufar shirinta na tallafa wa ‘yan kasa (N-SIP) shine inganta rayuwar talakan Najeriya Shirin nan na ciyar da daliban makarantun firamare da abincin da aka noma a Najeriya (HGSFP) ya yi mamaya zuwa jihohi 30 na kasar nan ya zuwa yanzu, kamar yadda wani jawabi daga fadar shugaban kasa ya bayyana.

Laolu Akande, babban mai taimaka wa mataimakin shugaban kasa a bangaren yada labarai, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, a Abuja. Ya ce, burin gwamnatin shugaba Buhari shine inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Ya bayyana cewar shirin tallafa wa ‘yan kasa (N-SIP) da gwamnatin tarayya ta bullo da shi, ya na matukar kawo canji mai kyau a rayuwar ‘yan Najeriya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Buhari da Osinbajo

Akande ya ce, yanzu haka dalibai miliyan 9.5 na cin moriyar shirin, sannan ya kara da cewa gwamnatin na da burin ciyar da dalibai miliyan 12 ne a karkashin shirin a jihohi 36.

Jihohin da yanzu haka ke cin moriyar shirin kamar yadda Akande ya lissafa su ne:

 1. Anambra
 2. Abia
 3. Akwa Ibom
 4. Adamawa,
 5. Bauchi,
 6. Benue,
 7. Borno,
 8. Kuros Riba,
 9. Ebonyi,
 10. Enugu,
 11. Kaduna,
 12. Kebbi,
 13. Kogi,
 14. Sokoto,
 15. Nasarawa
 16. Taraba,
 17. Ogun,
 18. Oyo,
 19. Osun,
 20. Filato,
 21. Delta,
 22. Imo,
 23. Kano,
 24. Jigawa,
 25. Katisna,
 26. Neja,
 27. Gombe
 28. Ondo
 29. Edo
 30. Zamfara.

Ya kara da cewa bayan ciyar da daliban, shirin ya samar da aiki ga masu girka abinci 101,913 a jihohin. Read more: https://hausa.legit.ng/1234085-gwamnatin-tarayya-ta-saki-jerin-jihohi-30-da-ke-cin-moriyar-shirin-ciyar-da-dalibai.html

Share This Post
Have your say!
00

Customer Reviews

5
0%
4
0%
3
0%
2
0%
1
0%
0
0%

Leave a Reply

Thanks for submitting your comment!