Dan gote

Mutumin da ya fi kowa tarin dukiya a nahiyar Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa, da a yanzu zai koma ya zama yaro matashi, akwai irin kasuwancin da zai yi, wanda ya sha bamban da wanda ya ke yi a halin yanzu, ya na mai bai wa matasan nahiyar shawarwari, idan su na son zama kamar shi, inda ya ce, hakan mai iya yiwuwa ne.
Hamshakin attajirin ya bayyana hakan ne lokacin wata hirar musamman da ya yi da attajirin nan dan kasar Sudan Mo Ibrahim a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa karshen makon jiya.
Wani mahalarcin taron ne ya tambayi attajirin ko wadanne bangarori zai fi mayar da hankali idan a ce ya na a matsayin dan shekara 21 da haihuwa ne a yanzu kuma ya na shirin fara kasuwanci?
Sai Dangote ya amsa da cewa, zai fi mayar da hankali ne a harkokin sadarwa na zamani da kuma aikin gona.
“Wadannan ne bangarori biyu da za su fi kawo riba,” in ji shi.
Sai dai daga nan ya ja kunnen matasa game da dabi’unsu bayan fara kasuwanci, musamman ‘yan Afirka.
Ya ce, “mu na kashe ribar da ba ta kai ga zuwa hannunmu ba. Da zarar ka fara kasuwanci kuma kasuwancin ya fara samun cigaba, maimakon ka yi ta kara uwar kudin, sai mutum ya fara kashe kudin da tunanin ribar za ta cigaba da zuwa.”
Ya cigaba da cewa, “dole ne mutum ya nutsu, saboda akwai kalubale nan da can.”
Attajirin ya ce, “bai kamata mutum ya fara kashe kudi ba-ji-ba-gani ba, saboda idan ka sayi manyan abubuwan more rayuwa (kamar motocin kawa) za su dauke ma ka hankali daga harkokin kasuwancinka.”
Daga nan, ya bayar da misali da kansa, inda ya ce, “ba ni da wani gidan shakatawa mallakina a ko’ina a fadin duniya, amma akwai wasu daga cikin ma’aikatana da su ke da gidan shakatawa a birnin Landan.”
Dangote ya bayyana cewa, ya taba zuwa banki, inda ya karbo Dala miliyan 10, domin ya tabbatar da cewa da gaske ya na da kudi. Ya ce, da ya je bankin, ya rubuta takardar karbar kudi, sai ya karbi kudin lakadan, sa’annan ya zuba su a bayan motarsa. Sai dai ba kashe kudin ya yi ba.
“Washegari na mayar da su banki, domin cigaba da ajiyarsu,” in ji shi, domin da ma ya amsi su ne saboda ya tabbatar ya na da su din, domin bai saba ganin kudi lakadan haka ba.
Da a ka tambaye shi nawa ya ke da shi a cikin aljihunsa a lokacin hirar, sai ya ce, “za ka yi mamaki. Babu ko sisi a aljihuna. Ko Dala daya babu a ciki.”
Dangote ya ce, aikin gina matatar man da ya ke yi a jihar Legas ta Najeriya zai ci kimanin Dala biliyan 12 zuwa 13. Ya ce idan a ka kammala gininta, za ta rika samar da gangar mai 650,000 a kowace rana.
Har wa yau, ya ce, idan a ka kammala aikinta, hakan zai mayar da Najeriya kasa ta biyu da ta fi fitar da albarkatun man fetur a yankin Kudu da Saharar Afirka.
“Babban kalubalen da mu ka fuskanta lokacin fara gina matatar mai shi ne, sai da mu ka gina tashar jirgin ruwa ta musamman, saboda babu wata tashar jirgin ruwa a kasar da za mu iya shigo da manyan na’urorinmu ta ita.”
A bangaren siminti, Dangote ya ce, a bana Najeriya za ta kasance kasar da ta fi kowacce fitar da shi a nahiyar Afirka.

SANARWA!

GobirOnline.com na bukatar Karin ma’aikata (Voluntary), kwararru, ta fannin watsa Labarai, Tarihi, wasanni da Al’adu, Domin bunkasa ayukkan wannan shafin.

CONTACT US

We're not around right now. But you can send us an email and we'll get back to you, asap.

Sending

©2019 GobirOnline  all right received | Arewa-community | G. D. A.

or

Log in with your credentials

or    

Forgot your details?

or

Create Account